Yaro Dan shekara 9 da yake samun naira biliyan 13 duk shekara a YouTube duba matakan dayabi kafin samun kudin>>> - UKCCV.COM --
Yaro Dan shekara 9 da yake samun naira biliyan 13 duk shekara a YouTube duba matakan dayabi kafin samun kudin>>>

Yaro Dan shekara 9 da yake samun naira biliyan 13 duk shekara a YouTube duba matakan dayabi kafin samun kudin>>>

>


Ryan mai shekaru 9, wanda yayi suna matuka a yanar gizo sakamakon tashar YouTube da yake da ita mai suna Ryan World, inda yake yin bita akan kayan wasan yara.


Tashar ta su da ya hada kai shi da iyayenshi suke tafiyar da ita, suna samun dala miliyan talatin da biyu ($32,000,000), kimanin naira biliyan sha uku (N13b) a kudin Najeriya, kamar yadda Celebrity Net Worth ta ruwaito.


A shekarar 2017 Tashar Ryan’s World ta zama tasha ta takwas da tafi kowacce samun kudi a duniya, kamar yadda jaridar Forbes ta ruwaito.


Ryan yaa fara wannan tasha ta shi a shekarar 2015, inda yake nuna kayan wasan yara shi da iyayen shi da kuma ‘yar uwarshi, wasu majiyoyin sun bayyana cewa, tun daga lokacin tashar ta cigaba da yaduwa kamfanunnuka suka cigaba da kawo musu tallar kayan wasan yara da sauran su.


Daga shekarar 2016 zuwa 2017 Ryan ya samu dala miliyann 11 na kudin shiga. A shekarar 2018, ya ninka kudin shi inda ya samu dala miliyan 22, a lokacin ya zama mutum da yafi kowa samun kudi a YouTube. Haka ya cigaba da yin suna har zuwa shekarar 2019, inda ya saamu dala miliyan 26, kamar yadda jaridar Forbes ta ruwaito. A shekarar 2020 Ryan ya samu dala miliyan 30, inda ya rike matsayinsa na mutum da yafi kowa samun kudi a YouTube a shekaru uku a jere.


Sakamakon wannan nasara da suka samu, wata tasha mai suna Sunlight Entertainment, ta samu dauki nauyin haska bidiyoyin su.


Banda Tashar shi ta YouTube, Ryan kuma ya samu dala miliyan 200 daga wajen kamfanoni da yake yi musu talla, a rahoton da jaridar The Guardian ta fitar. Tashar Nickelodeon ma sunyi yarjejeniya da yaron inda za su dinga haska bidiyon shi mai dogon zango.


An yiwa tashar YouTube ta Ryan’s World, inda mujallar Celebrity Net Worth ta bayyana cewa tashar akalla za ta kai dala miliyan dari biyar ($500,000,000).NEW YORK, NEW YORK – FEBRUARY 24: Gabrielle Green, Brian Robbins, Nathan Janak as Ariana Grande on “All That”, Bob Bakish, Ryan Kaji, Young Dylan and Josh Dela Cruz attend the Nickelodeon Exclusive Presentation at The Shed on February 24, 2020 in New York City. Photo: Photo by Astrid Stawiarz/Getty Images for Nickelodeon

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa


Source: Labarun Hausa

0 Response to "Yaro Dan shekara 9 da yake samun naira biliyan 13 duk shekara a YouTube duba matakan dayabi kafin samun kudin>>>"

Post a Comment