Kalli Kasaitattun Bidiyoyi da Hotunan 'Bridal Shower' na Zarah Bayero da Yusuf Buhari - UKCCV.COM --
Kalli Kasaitattun Bidiyoyi da Hotunan 'Bridal Shower' na Zarah Bayero da Yusuf Buhari

Kalli Kasaitattun Bidiyoyi da Hotunan 'Bridal Shower' na Zarah Bayero da Yusuf Buhari

>


Hotuna da bidiyoyin wankan amarya, Gimbiya Zahra Bayero da Yusuf Muhammadu Buhari sun fara bayyana A bidiyoyin da hotunan, 


an ga zukekiyar gimbiyar sanye da rigar alfarma yayin da kasaitattun kawayenta ke kewaye da ita Walkiya, kyalli, kyau, izza da kasaitar tsuleliyar amaryar ya cika ko ina yayin da take sanye da farar riga mai hannayen raga 


Kano - Alamu bayyane suke na cewa tuni aka fara shagalin bikin gidan shugaban kasa da na gidan sarautar Bichi. Tun a ranar Asabar da ta gabata Legit.ng ta fara kawo muku kyawawan hotunan wasan Polon da aka yi a ranar Juma'a da ta gabata na bikin diyar Sarkin Bichi, Gimbiya Zahra Bayero da dan shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari. 


A yau kuwa Legit.ng ta tattaro muku tsula-tsulan hotuna da bidiyoyin wankan amarya, wanda a zamanance aka mayar da shi liyafa mai zaman kanta da ake kira da Bridal Shower. 
A cikin bidiyoyin da hotunan da shafin @arewafamilyweddings suka wallafa, an ga kyakyawar gimbiyar tare da kawayenta suna ta daukan hotuna yayin da sauti mai dadi ke tashi. 
Ya kwalliyar amarya da kawayenta ta bayyana? A hotunan, da bidiyon, an ga tsuleliyar amaryar sanye da farar riga mai hannuwan raga yayin da kawayenta ke sanye da riguna farare na ankon da aka yi shi domin wankan amaryan.  


Walkiya, kyau tare da izzar amarya jinin sarauta, ta cika wurin da ake liyafar, duk da dai kawayenta da kallo daya zaka musu ka san 'ya'yan wane da wance ne suma ba a bar su a baya ba. 0 Response to "Kalli Kasaitattun Bidiyoyi da Hotunan 'Bridal Shower' na Zarah Bayero da Yusuf Buhari"

Post a Comment