Bam ya tarwatsa yan Shi'a yayin Muzaharar Ashura, mutum 50 sun jikkata duba yadda abin ya faru - UKCCV.COM --
Bam ya tarwatsa yan Shi'a yayin Muzaharar Ashura, mutum 50 sun jikkata duba yadda abin ya faru

Bam ya tarwatsa yan Shi'a yayin Muzaharar Ashura, mutum 50 sun jikkata duba yadda abin ya faru

>


Akalla mutum uku sun rasa rayukansu yayinda mutum 50 suka jikkata yayinda Bam ya tashi a tsakiyar mabiya akidar Shi'a yayin Muzahara a birnin Pakistan, cewar hukumomi.


Aljazeera ta ruwaito wani babban jami'in gwamnatin birnin Bahawalnagar da cewa: "Muna masu tabbatar da labarin cewa mutum uku sun mutu yayinda 50 suka jikkata a tashin Bam." 


A shafukan ra'ayi da sada zumunta, an ga bidiyoyin mummunar tashin Bam din yayinda jama'a ke kokarin taimakon wadanda suka jikkata. Wani jami'in dan sanda, Kashif Hussain, ya tabbatar da wannan abu ga AFP. Yace: 


"Har yanzu bamu san yadda abin yake ba amma muna cigaba tattara bayanai daga wajen." 0 Response to "Bam ya tarwatsa yan Shi'a yayin Muzaharar Ashura, mutum 50 sun jikkata duba yadda abin ya faru"

Post a Comment