Zanbar Musulunci idan har Al-ummar Musulmi Basu taimakeni ba, -Cewar Wani Matashi Dan Jihar Jigawa - UKCCV.COM --
Zanbar Musulunci idan har Al-ummar Musulmi Basu taimakeni ba, -Cewar Wani Matashi Dan Jihar Jigawa

Zanbar Musulunci idan har Al-ummar Musulmi Basu taimakeni ba, -Cewar Wani Matashi Dan Jihar Jigawa

>

 


A wani rubutu da muka samo daga shafin yanar gizo na Facebook na Datti Assalaffiy, ya bayyana cewa akwai wani matashi da alamu suka nuna cewa ya fito daga jihar Jigawa wanda ke kokarin yin ridda ya fice daga addinin Musulunci.


Ya ce matashin mai suna Abba yana kokarin ficewa daga addinin Musulunci, saboda a cewar shi tunda ya taso babu wani amfani da addinin Musulunci ya kara masa.


Na bada kwanaki kadan a nuna mini alfanun Musulunci

Saurayin ya ce ya bada kwanaki kadan idan har al’ummar Musulmi ba su nuna masa wani abin amfani a cikin addinin Musulunci ba, haka kuma idan har gwamnatin Najeriya ba ta bashi babban mukami ba zai yi sallama da addinin Musulunci, kamar dai yadda ya bayyana hakan a wani bidiyo da ya sanya a shafinsa na Facebook.Kamar yadda shafin na Datti Assalafiy ya wallafa, saurayin ana kyautata zaton ya fito daga jihar Jigawa.


Na karance Qur’ani baki daya banga wani amfaninsa ba

Kamar yadda saurayin ya bayyana, ya karance Al-Qur’aani mai girma baki data amma bai ci karo da inda ya kara masa amfanin komai ba sai tashin hankali.


A cewar Datti Assalafiy:


A maganganun yaron akwai yiwuwar dan kwangilar Yahudawa ne ko kuma yana da tabin hankali, ko kuma ya shiga addinin maguzawa na “Atheist”, wanda suke cewa babu Allah baki daya.


Amma ina kyautata zaton yana da tabin hankali, saboda ya ce dole sai gwamnati ta bashi mukami kafinn ya cigaba da zama a addinin Musulunci, wannan magana daa yayi tana kama da ta mutumin da ya samu matsalar kwakwalwa


Datti AssalafAssalafiy

 

A taimaka a kai masa dauki domin yana neman taimako, cewar Datti AAssalafiy


Ya kara da cewa idan har akwai mutanen da suke da masaniya da matashin saurayin ko kuma suka san ‘yan uwaansa, su taimaka su fargar da su domin suyi duba da abinda matashin saurayin ke yadawa a shafinsa na Facebook, inda ya ce idan har matashin ba shi da lafiya su hana shi hawa shafin Facebook su kuma fita su nema masa magani.


Ashe dai ya samu tabin hankali ne a lokacin da yaje karatu kasar waje
Sai dai kuma wani matashi mai suna Comrd Abba Hassan, ya bayyana cewa ya san matashin saurayin, inda har ya kara da cewa abokine a wajen su.

Abba ya ce saurayin ya samu tabin hankali, sakamakon shaye-shaye da yaje yayi a kasar Uganda lokacin da yaje yin karatu can.

Wanan bawan Allah dai abokinmune kuma dan unguwarmune unguwar agumau Hadejia jigawa kuma yasamu tabin hankali sakamakon shayeshaye dayayi a kasar Uganda lokacin da yajekaratu can

Comrd Abba Hassan

0 Response to "Zanbar Musulunci idan har Al-ummar Musulmi Basu taimakeni ba, -Cewar Wani Matashi Dan Jihar Jigawa"

Post a Comment