Yanzu yanzu: Ɗan Kasar Denmark wanda ya yi zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad (S), ya mutu - UKCCV.COM --
Yanzu yanzu: Ɗan Kasar Denmark wanda ya yi zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad (S), ya mutu

Yanzu yanzu: Ɗan Kasar Denmark wanda ya yi zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad (S), ya mutu

>


Mai zanen shaguben nan a jarida dan kasar Denmark Kurt Westergaard, wanda aka fi saninsa saboda zanen da ya yi na Annabi Muhammad (SAW) wanda ya janyo ce-ce-ku-ce, ya mutu.


Ya mutu yana da shekarun 84.


An wallafa zanen ne a shekara ta 2006, kuma fafutikar da Musulmi masu raji suka yi ta kai ga zanga-zanga wadda ta rikide ta zamo tashin hankali a kasashe da dama na Musulmai.


A baya an yi hakon Westergaard don kashe shi, kuma ala tilas ya arasa rayuwarsa a wani mazauni na sirri tare da kariyar 'yan sanda.


Sake wallafa zanen a mujallar nan ta zambo ta kasar Faransa wato Charlie Hebdo a shekarar 2015 ya sa an kai wa ofishinta hari inda masu kishin Islama suka kashe mutane 12.


Rahotan Bbc Hausa

0 Response to "Yanzu yanzu: Ɗan Kasar Denmark wanda ya yi zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad (S), ya mutu"

Post a Comment