Kalli Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu - UKCCV.COM --
Kalli Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu

Kalli Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu

>


A ranar Juma'a aka fara shagalin bikin auren Yusuf Buhari da Zarah Bayero An fara shagalin ne da wasan kwallon Polo wanda amarya da angon suka halarta An ga ango Yusuf sanye da rigar wasan yayin da amarya Zarah ta saka bakar riga Kano 


Rahotannin da Legit.ng ta fara tattarowa shine na fara shagalin bikin da daya tilo na shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari da diyar sarkin Bichi, Alhaji Nasir Bayero. Kamar yadda shafin @insidearewa ya wallafa a daren ranar Juma'a, an ga hotunan amarya Zarah Bayero tare da angonta Yusuf yayin da ake gasar kwallon Polon bikinsu.


Wannan alama ce ta yadda aka fara shagalin bikin a ranar Juma'a duk da za a yi asalin daurin auren a farkon watan Augusta. 


Gwamnoni, ministoci da jiga-jigan gwamnati ne suka je neman aure A cikin watan Yuli ne tawagar gwamnoni, ministoci da kuma jiga-jigan 'yan siyasa wadanda suka samu jagorancin Gwamna Badaru na jihar Jigawa suka dira a birnin Dabo domin nemawa Yusuf Muhammadu Buhari aure Gimbiya Zarah Bayero. 

An kai lefen Zarah Bayero a watan Yuli Har ila yau, duk a cikin watan ne mata suka kai akwatunan aure dankare da kaya na lefen gimbiya Zarah Bayero. Kamar yadda aka tattaro, biyu daga cikin akwatunan na dankare da zinari da lu'u-lu'u da kuma tsabar kudi. 


Source: Legit

0 Response to "Kalli Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu "

Post a Comment