Ina neman miji ruwa a jallo, kyakkyawar budurwa ta koka kan rashin miji - UKCCV.COM --
Ina neman miji ruwa a jallo, kyakkyawar budurwa ta koka kan rashin miji

Ina neman miji ruwa a jallo, kyakkyawar budurwa ta koka kan rashin miji

>


Wata kyakkyawar budurwa da ke rajin kare hakkin mata, ta fito ta janye maganar a wani sabon bidiyo, inda aka nuno ta cikin hawaye.


Budurwar wacce ba ta bayyana sunanta ba, ta bayyana cewa ta neman miji ruwa a jallo, saboda tana kewar aure, haka kuma tana son haihuwa.


A cewar budurwar, tana kishin ganin mata da mazajensu suke kula da su sosai.


Ta gano cewa akidar da take dashi ta kare hakkin mata, na daya daga cikin dalilin da ya sanya maza basa son kusantar ta, inda ta yanke shawarar ajiye wannan akida.


A cewar ta:

Ina kewar aure da rashin yara, yanzu kuma na kai matsayin da ina jin bakin ciki sosai, ina kishin naga ma’aurata suna zaune lafiya cikin farin ciki, saboda mazajensu ba sa yaudarar su.. Ina ganin maza sune komai a rayuwa. Yaanzu ne nake ganin wannan kuma, saboda na san ba zan iya rayuwa ba namiji ba.


Cewar budurwar


 Irin mijin da take burin samu

Kyakkyawar budurwar ta ce ita ba ta damu ba idan namijin mai kudi ne ko talaka, haka kuma ba ta da damuwa idan dogo ne ko gajere, ta kara da cewa ita abinda take bukata shine namiji wanda yake numfashi.


Ta ce:

Ban damu ba idan kai mai kudi ne ko talaka, gajere ko dogo, kyakkyawa ko mummuna, duk ban damu da wannan ba, matukar kai namiji ne mai numfashi. Shine iya abinda nake nema, ina so ne saboda ina matukar neman mijin aure. Ina cikin matukar damuwa.


Budurwar

Budurwar ta yi alkawarin yiwa mijinta biyayya, ta ce za ta yi duk abinda ya saka ta, hatta kayan shi ita ce za ta dinga wankewa.


Budurwar ta hau shafin Twitter tana neman mijin aure

A shekarar da ta gabata ne dai wata kyakkyawar budurwa Bahaushiya da ta bayyana sunanta da Salmerh Umar ta hau shafin sadarwa na Twitter tana neman mijin aure, inda ta nemi ‘yan Najeriya su taya ta da addu’a.


Budurwar mai sunan @SalmerUmar a shafin Twitter ta bayyana cewa ba za ta iya boye damuwar ta ba.


Salmerh, wacce ta fito daga jihar Gombe, ta wallafa hotunanta guda biyu a shafin na sadarwar, domin ta nunawa mutane irin baiwar kyau da Allah ya ba ta.

0 Response to "Ina neman miji ruwa a jallo, kyakkyawar budurwa ta koka kan rashin miji"

Post a Comment