Hukumar Ganduroba Ta Yi Magana Kan Halin da Sheikh AbdulJabbar Yake Ciki a Gidan Yari - UKCCV.COM --
Hukumar Ganduroba Ta Yi Magana Kan Halin da Sheikh AbdulJabbar Yake Ciki a Gidan Yari

Hukumar Ganduroba Ta Yi Magana Kan Halin da Sheikh AbdulJabbar Yake Ciki a Gidan Yari

>Hukumar jami'an dake tsaron gidan gyaran hali ta jihar Kano, ta musanta rahoton dake yawo cewa sheikh Abduljabbar Kabara yana cikin mawuyacin hali a gidan yari, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito


Shehin malamin wanda ya yi ƙauran suna wajen kawo maganganun dake jawo cece-kuce yana gidan yari biyo bayan umarnin kotu. 


Kakakin hukumar, DSC Musbahu K/Nassarawa, yace rahoton dake yawo cewa malamin bashi da lafiya ƙaryane. 


Yace: "An jawo hankalin hukumar mu reshen jihar Kano kan wasu ƙarerayi da ake yaɗawa cewa, Sheikh Abduljabbar Kabara, wanda yake tsare a hannun mu, yana cikin matsananciyar rashin lafiya." 


Malamin yana cikin ƙoshin lafiya DSC Musbahu ya ƙara da cewa shehin malamin tare da sauran yan fursuna dake hannunsu, suna cikin ƙoshin lafiya. 


Yace: "Muna kira ga mutane da su yi watsi da wannan karyar da bata da tushe ballantana makama, wadda aka shiryata domin wani dalili."


"Muna tabbatar wa al'umma cewa Sheikh, tare da sauran yan fursuna dake tsare a gidajen yarin mu suna cikin ƙoshin lafiya." 


"Kuma hukumar mu tana bada muhimmanci matuka ga lafiyar dukkan yan fursuna dake hannunta." 

0 Response to "Hukumar Ganduroba Ta Yi Magana Kan Halin da Sheikh AbdulJabbar Yake Ciki a Gidan Yari "

Post a Comment