Kalli Bidiyon wani mutum mai mata 43 da yara sama da 200, ba a lissafa da yaransa mata ba - UKCCV.COM --
Kalli Bidiyon wani mutum mai mata 43 da yara sama da 200, ba a lissafa da yaransa mata ba

Kalli Bidiyon wani mutum mai mata 43 da yara sama da 200, ba a lissafa da yaransa mata ba

>


An gano wani mutum mai mata da yawa a wani gari da ake kira Tenzuku a yankin Gabashin kasar Ghana inda yake da ‘ya’ya sama da 200 


Da yake magana a wani karamin taron yaran da ke wurin, mai magana da yawun mutumin ya nuna cewa mutumin na da mata 43 


An ruwaito cewa adadin yaran da aka bayyana sun yi kasa da ainihin adadin saboda ba a kidaya yara mata ba 


An gano wani mutum wanda aka bayyana sunansa da Nana yana da yara sama da 200 tare da matansa 43 a yankin Gabashin Ghana. 


Shirin safe na Angel TV (Anopa Bofo) ƙarƙashin jagorancin Kofi Adomah sun yi tattaki zuwa Tenzuku, ƙauyen da ake tukin awowi 13 daga Accra don yin hira da wasu daga cikin yaran babban gidan. 


Kodayake mutumin da kansa bai halarci taron ba, amma mai magana da yawunsa ya nuna cewa kimanin matan da yaran da aka kiyasta ba su kai ainihin adadin ba.


Kalli cikakken bidiyon a kasa A cewarsa, ba a kirga yawancin ‘ya’yansa mata saboda da zarar sun yi aure, sai su koma zama tare da mazajensu. 


'Yan asalin Tenzuku suna koina Ya kuma bayyana cewa da wuya a sami wani wuri a Ghana da babu ɗan asalin Tenzuku, saboda da yawa sun yi kaura zuwa sassa daban-daban na ƙasar. 


Akwai zaman lafiya Mutumin ya kuma tabbatar da cewa dukka ahlin suna zaune lafiya, suna cin abinci daga junansu sannan kuma suna kula da ya’yan juna, duk da yawansu. 


0 Response to "Kalli Bidiyon wani mutum mai mata 43 da yara sama da 200, ba a lissafa da yaransa mata ba"

Post a Comment